Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Hannuntawa Uzbekistan Jiragen Tsohuwar Gwamnatin Afghanistan


Gwamnatin Taliban ta Afghanistan da ke ganin jiragen na kasar ta Afganistan ne, sun ki amincewa da mika su ga Uzbekistan.

Amurka ta mikawa gwamnatin kasar Uzbekistan jiragen da tsoffin sojojin saman Afghanistan suka hau zuwa kasar Uzbekistan bayan da Taliban ta kwace iko da birnin Kabul a shekarar 2021.

Wani mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka, ya fadawa Muryar Amurka a ranar Alhamis cewa, an hannunta mallakar "wasu jirage" ga Uzbekistan a wani bangare na shirin ma’adanar Ma'aikatar Tsaro.

Kakakin ya shaidawa Muryar Amurka ta wani sakon email cewa, "an amince da mika jiragen ne bisa yarjejeniyar hadin gwiwar da muke da ita a fagen yaki da ta'addanci, da miyagun kwayoyi, da kuma inganta tsaron kan iyaka," amma bai bayyana adadin jiragen da aka mika wa gwamnatin ta Uzbekistan ba.

Makomar jiragen da aka kai kasar Uzbekistan bayan da kasar Afganistan ta fada hannun 'yan Taliban, ya kasance wata takaddama tsakanin Taliban da Uzbekistan tsawon shekaru uku da suka gabata.

Sojojin saman Afghanistan sun dauki kusan jiragen sama 46, da suka kumshi jiragen soji 22 da jirage masu saukar ungulu 24 - zuwa Uzbekistan, yayin da gwamnati a Afghanistan ta durkushe a lokacin da kungiyar Taliban ta ke dada matsawa a watan Agustan shekara ta 2021.

'Yan Taliban wadanda ke ganin jiragen na Afganistan ne, sun ki amincewa da mika su ga Uzbekistan.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG