Sabuwar Na'urar Fallasa Ta'addanci

Hukumomi a kasar Jamus, sun kaddamar da wata sabuwar na’urar gwaji, wadda zata dinga amfani da yanayin jikin mutun, don bayyanar da ko wanene mutun. Na’urar dai za’a dinga amfani da itane wajen magance ayyukan barna da ta’addanci.

Yadda na’urar zata dinga aiki shine, idan mutun ya taba zuwa wani waje, idan kyamara ta dauki hoton mutun koda kuwa ya rufe fuskar shi, na’urar zata bayyanar da ko wanene, ta yadda jikin mutun yake ba lallai sai anga fuskar shi ba.

An dasa na’urar a tashar jirgin kasa dake babban birnin Berlin, inda mutane dari biyu 200, suka bada hotunan su da sunan su don yin gwaji da su a karon farko. A cewar ministan harkokin cikin gidan kasar Mr. Thomas De Maiziere, yace kimiyya da fasaha zata zama hanya daya tilo, da za’a iya magance duk wasu ayyukan barna a cikin al’umah.

Ana sa ran idan wannan tsarin yayi nasara, sauran kasashe ma a duniya zasu dauki wannan sabon salon, wajen gano mutane da suke barna a cikin al’umah. Ita dai na’urar zata taimaka matuka wajen rage barna, a duk inda aka saka na’urar kyamara da zata dinga daukar kai kawon mutane.