Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Apple Ya Sayi Manhajar Tantance Wakoki "SHAZAM"


Kamfanin Apple ya sayi manhajar tantance wakoki da ake kira Shazam wadda aka kirkiro a Birtaniya, wanda ke zama babban ciniki da Apple ya taba yi.

Ita dai Shazam fasaha ce da ke baiwa masu amfani da ita damar tantance wakokin da suka ji a gidajen radiyo ko wasu kafofi na daban. Apple dai ya ce manhajar zata samu shiga cikin sauran kayayyakin da yake sayarwa na wakoki.

A cewar mai magana da yawun kamfanin Apple, “Tun lokacin da aka kaddamar da runbun mahajoji na Apple da ake kira App Store, Shazam ya zamanto ‘daya daga cikin manhajojin da suka yi fice. Wanda a yau, miliyoyin mutane suna amfani da ita a duk fadin duniya, kan kafofi daban-daban.

An kirkiro manhajar Shazam a shekarar 1999 kuma ta samu habaka lokacin da aka fitar da runbun manhajojin Apple na iPhone App Store a shekara ta 2008, inda take samun kudin shiga ta hanyar aika mutane su sayi wakoki a iTune.

Ya zuwa yanzu dai babu tabbacin yadda Apple yake shirin yin amfani da Shazam a kafarsa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:08 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG