Wannan doka ce da ta kawo sauye-sauye a fannin biza da matafiya za su yi amfani da ita kuma wacce ta zo daidai da zamani a cewar hukumomin kasar.
Shugaban Hukumar shige da fice Mohammed
Babandede ya yi bayani cewa matafiya da za su shigo Najeriya daga wasu kasashe su ne za su samu biza kai-tsaye a daidai lokacin da suka shigo kasar kwatankwacin yadda ake yi wa ‘yan Najeriya a kasar da suka fito sannan a daidai yawan kudin da ‘yan Najeriya ke biya a wadancan kasashen.
Babandede ya ce ministan ma'aikatar shige da fice Ogbeni Ra'uf Aregbesola shi ne ya ba da umurnin daukan wannan mataki.
Tuni wannan mataki ya fara daukan hankulan ‘yan Najeriya irinsu mai sharhi Hajiya Mariya Ibrahim Baba wacce ta ce lallai matakin yana da kyau kuma zai sa harkar biza a Najeriya ta zama daidai da kasashen da suka ci gaba.
Amma ta nuna fargabar cewa kasar na fama da rashin wutar lantarki kuma ga karin da aka yi a fanin man fetur da ka iya gurgunta hanyoyin samu sadarwa da za a yi amfani da na'urori masu aiki da kwakwalwa.
A nashi nazarin, kwararre a fanin zamantakewan dan Adam kuma Malami a Jami'ar Abuja Dokta Abubakar Umar Kari ya ce tsari ne da zai taimaka wa kasa wajen samun kudaden shiga a daidai lokacin da ake kukan rashin kudi a sakamakon bular cutar COVID-19.
Your browser doesn’t support HTML5