Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kafa wani kwamiti da zai nemi maslaha kan haramta bizarta da Amurka ta yi ga wasu rukunan ‘yan Najeriya.
Mai taimakawa shugaban Najeriya kan harkar yada labarai Femi Adesina ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Kwamitin zai gudana ne karkashin Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, wanda zai yi nazari tare da tabbatar da an sabunta sabbin ka’idojin da Amurka ke bukata a bi, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
“Najeriya a shirye take ta ci gaba da karfafa dangantakarta da Amurka da sauran kasashen duniya, musamman ma kan abin da ya shafi tsaro,” jaridar US News ta yanar gizo ta ruwaito Reuters.
A ranar juma’a ma’aikatar tsaron cikin gida ta Homeland Security ta Amurka ta fitar da jerin kasashe shida da za ta rika hana su visar shiga kasar.
A cewar hukumomin Amurka, kasashen sun gaza samar da matakan tsaro da za su gamsar da Amurkar.
Matakin dai bai yi wa hukumomin Najeriya dadi ba.
Sai dai babban abokin hamayyar Shugaba Buhari a zaben 2019, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi kira ga Amurka da ta sake duba wannan mataki da ta dauka.
A wani sakon Twitter da ya wallafa a shafinsa, Atiku ya yi kira ga Amurka da ta bar haramcin akan jami'an gwamnati kadai.
“Ina sake kira ga Shugaba @realDonaldTrump da ya dauki matakan da za su kaikaici jami’an gwamnati kadai wadanda suka gaza yin ayyukansu, maimakon daukacin ‘yan Najeriya.”
Baya ga Najeriya, sauran kasashen da aka haramta masu bizar sun hada da Eritrea, Kyrgystan, Myanmar, Sudan da kuma Tanzania.
Sai dai a bangaren Najeriya, haramcin ba da bizar bai shafi dalibai, masu yawon bude da kuma neman lafiya ba.
Matakin ya shafi masu sha’awar zuwa su zauna ne a kasar a matsayin zama na dindindin, ko masu neman bizarLottery ko wadanda wasu kamfanoni ko ma’aikatu za su ba su aiki.