Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zamu Maida Martani A Kan Duk Kasar Da Ta Hana 'Yan Najeriya Biza


Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari

Ma’aikatar shige da fice a Najeriya ta ce ta kimtsa domin fara aiki a filayen saukar jiragen saman kasa da kasa yayin da jiragen kasashen suke fara aiki zuwa Najeriya, bayan da kasar ta bi sahun sauran kasashen duniya a yaki da annobar coronavirus.

Shugaban ma’aikatar shige da ficen ta Najeriya Muhammad Babandede ya ce ma’aikatar sa ta shirya tsaf domin yin aiki a kan fasinjoji da zasu sauka a manyan filayen saukar jiragen saman kasar guda biyu da suka hada da na Lagos da na babban birnin tarayya Abuja, a daidai wannan lokaci da jiragen waje suka fara shigowa Najeriya.

A wata hira ta musmman da Muryar Amurka, Babandede ya tabbatar da cewa an dauki kwararan matakan da suka dace game da cutar coronavirus a filayen saukar jiragen saman. Ya ce sun kare ma’aikatan su daga kamuwa da COVID-19.

Ya ce gwamnati ta fitar da sabuwar doka cewa kafin fasinja ya shiga jirgi sai ya yi gwajin cutar kafin ya iso Najeriya kuma duk wanda bai bi wannan doka ba za a hukunta shi, ko wanene koda kuwa dan Najeriya ne kuma haka zai kare ma’aikatan mu da zasu biciki fasfunan fasijojin.

Shugaban ma’aikatar shige da ficen ya ce akwai kuma matakai da ma’aikatar sat a dauka da hadin gwiwar ma’aikatar harkokin cikin gida game da ba ‘yan kasar waje mazauna Najeriya na cikin gida da waje da takardun bizar su ta kare ko kuma zata kare daman gyara takardun su, abinda ya kira sauki da hukumomin Najeriya suka yiwa mutane.

Sai dai ya kara da cewa Najeriya zata maida martani a kan kasar da ta hana ‘yan Najeriya bizar shiga kasarta saboda sabuwar bizar da shugaban kasa ya wallafa ta NVP2020 .

A cewar Muhammad Babandede, manyan filayen saukar jirage biyu kadai ne aka bude domin fara jigilar fasinjojin kasashen waje kuma a hankali za a bude sauran filayen sauka da tashin jiragen saman kasa da kasa a Najeriya.

Ga tattaunawar da Sale Shehu Ashaka ya yida Muhammad Babandede:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG