Kwamishanan 'Yansandan Imo ya Nemi Hadin Kan Jama'ar Jihar

Rundunar 'Yansandan Najeriya

Kwana kwanan nan aka sake ma kwamishanonin 'yansanda a Najeriya guraben aiki. Wanda aka kai jihar Imo ya nemi hadin kan jama'ar jihar da wasu hukumomin tsaro.
Sabon kwamishanan 'yansandan jihar Imo Alhaji Abdulmajid Ali ya kira jama'ar ta Imo da su bashi hadin kai da goyon baya domin kawar da bata gari a jihar.

Alhaji Abdulmajid Ali sabon kwamishanan ya bayana hakan ne a Owerri babban birnin jihar a wani taro na manema labarai jin kadan da kama aiki inda yace "Na kama aiki shekaranjiya na zo na kama aiki a nan jihar Imo...Shirin da na gani daga wanda na karbi aiki a hannunsa Alhaji Muhammed Katsina na ga akwai aiki cikakken da ya yi nawa kari ne na cigaba bisa ga abun da na gani a kasa...Zamu cigaba daga inda shi ya tsaya"

Daga bisani kwamishanan ya yi kairan neman hadin kai tare da sauran hukumomin tsaro na jihar da 'yan banga da jama'a jihar yacce "Zan nemi hadin kai ta mutanen jihar Imo, su bani cikakken hadin kai kamar yadda aka ba shi Malam Katsina...Ayyukan da yake faruwa kaman laifukan sace sace da ake tayi, dama akwai unit da suk incharge tare da hadin kan da muka samu na 'yan banga wadanda dama da su ake aiki" Yace zasu cigaba da aiki dasu da sauran hukumomin tsaro.

Wasu mazauna jihar sun furta ra'ayinsu game da kiran da kwamishana din yayi.Wani yace abun yabawa ne saboda haka suna murna da yunkurin da sabon kwamishanan 'yansandan ya fito dashi. Yace a shirye suke su bada hadin kai da goyon baya domin kawar bata gari daga jihar.

Wani kuma ya gargadi mutane su yi kusa da 'yansanda domin suna taimakawa wurin dakile satar mutane ko yin garkuwa da su.

Your browser doesn’t support HTML5

Sabon Kwamishanan Yansandan Imo ya Nemi Hadin Kan Jama'ar Jihar - 2:30