Shugabannin siyasa da na addini da na al'umma da kunugiyoyi sun fara tunanin abubuwanda suke so taron ya tattauna a kai. Sabili da haka ne matsan PDP suka yi taron nuna goyon baya ga taron kasa kodayake wasu na ganin taron zai zama dandali ne na haddasa kiyayya.
Alhaji Mai Basira shugaban matasan PDP bai yadda taron zai zama dandalin haddasa kiyayya ko raba kawunan kasa ba. Yace kwamitin da kwamnati ta kafa ya zagaya duk fadin kasar. Ya gana da 'yan siyasa da ma'aikata da shugabannin addinai da 'yan kasuwa da dalibai da matasa babu wanda aka bari domin su kawo abubuwan da suke so a tattauna a wurin taron.
Shi kuwa Pastor Simon Donli na kungiyar Kiristoci ta Najeriya yace ya dace taron ya kula da matasa wajem buda masu hanyar shiga gwamnati domin su matasan su ne zasu gaji shugabannin yau.Yace hatta shugaban kasa ya ce ana taron domin matasa ne idan ko haka ne to ya kamata su yi dumu dumu a cikin taron.
Shugaban Izala a jihar Gombe Uztaz Salisu Gombe yace yaki da talauci ta hanyar samarda hanyoyin dogaro da kai shi ne ya dace shugabannin al'umma a kowane mataki su mayarda hankali a kai. Kamar yadda shugaban kungiyar Izala na kasa Sheikh Bala Lau ya yi na kirkiro ma matasa aikin yi haka ya kamata taron kasa ya tanadi hanyoyin da za'a koyawa matasa ayyukan yi domin ba za'a samu zaman lafiya ba sai da aikin yi.