Alkalumma sun nuna cewa Najeriya ce kasa ta shida mafi arzikin man fetur a duniya banda dimbin albarkatun ma'adanan kasa da Allah ya baiwa kasar. To sai dai kusan kullum talakawa na dada talaucewa masu kudi kuma sai kara kudancewa suke yi yayin da suke sake tsuke bakin aljihu domin gudun kada arzikinsu ya ragu. Sai dai wasu sun kwatanta lamarin da yin rowa.
Idan ba'a yi hankali ba ikirarin da Najeriya ke yiwa kanta cewa ita ce giwar Afirka ka iya zama tarihi kamar yadda masana tattalin arziki da zamantakewar mutane ke harsashe. El-Haroun Mohammed malami a kwalajin ilimin kimiya da fasaha na Kaduna cewa ya yi "Ta ina ne aka zama giwar Afirka?" Kasar da bata da isashen wutan lantarki ina zata?
Dr Bashir Kurfi na Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria ya danganta rashin ingantar tattalin arzikin a siyasance da rashin adalci da kan sa fitina da rikici a ciki al'umma don basa iya noma ko fatauci sai yin gulma. Ta ce "To duk kasar da bata justice yanzu kai Malam Nasiru da ace san da aka kashe Sardauna Nzegwu shi Ironsi yayi trial nasu an 'executin' nasu da za'a yi asarar one million people?"
Dr Bashir Kurfi ya cigaba da cewa "Mohammed Yusuf din nan da aka kamashi aka harbeshi da ka kira police din ka yi executin nashi yadda law yace. Da za'a yi Boko Haram?Ko dama ka bari an yi free and fair election ya ci da za'a yi Boko Haram?"
To sai dai masu mulki nada nasu ra'ayin da ya sha ban ban da na masana kamar su Dr, Kurfi. Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Ramalan Yero na ganin barwa gwamnati hakin komai ke kawo komabaya da da kuma rashin tattaunawa da yin mahawarori.
Shi kuwa gwamna Ibrahim Hassan Dankwanbo na jihar Gobe wanda asalinsa babban akanta ne ya ce ba don kadara ta shigo da shi siyasa ba da ya juya ya cigaba da sana'arsa. Yace "Siyasa ba sana'a ba ce. Wannan abun da kuke yi kafintan nan shi ne sana'ar gaskiya...Bayan na zo takara na tara malamai ina neman gudunmawa. Malami na farko ya tashi yayi kamar minti goma. Kafin na ukun nan ya gama bana ma jin abun da yake fada. Hankali na ya tafi wani wuri. Wallahi ba dan na yi resigning ba da na koma...."
Gwamnoni na cewa a basu goyon baya don zasu yi kaza da kaza talakawa kuma na cewa an shasu sun warke a daina yi masu zane kan ruwa.