Wannan mugun harin yayi sanadiyar mutuwar mutane fiye da dari da suka hada da mata da yara da tsofofin mata da asarar dukiyoyin miliyoyin nerori. Gwamnatin tace abun da ya faru abun takaici ne kuma abun bakin ciki ne ganin yadda ake cigaba da asarar rayuka musamman ma ga mazauna kauyuka da basu ci ba ba su gani ba.Gwamnatin tace tana nan tana kokarin kai kayan agajin gaggawa ga wadanda bala'in ya shafa.
Mai baiwa gwamnan shawara kan harkokin yada labarai Alhaji Isa Umar Gusau yace akwai agajin da ake turawa kuma za'a kara turawa. Ya kara da cewa wannana abun da ya faru "ya bakantawa gwamna Kashim Shettima rai kuma akwai matakai da ake dauka wanda da yadda Allah za'a shawo kan wannan lamari"
Gwamnan jihar ta Borno tuni ya gana da shugaban kasar Najeriya Ebele Goodluck Jonathan tare da wasu masu ruwa da tsaki a harkokin tsaro kan hanyoyin da za'a bi domin dakile wannan matsala dake neman zama karfen kafa ga al'ummar jihar.
Alhaji Isa Umar Gusau ya kara haske kan abubuwan da suka taso bayan hare-haren na Izige. Yace "Mun ji wani rahoto a wata kafar watsa labarai da bana son in bayyana inda aka yi nuni da cewa an kashe mutane tamanin mabiya wani addini. Gaskiya wannan abun ya tayar mana da hankali kwarai kuma ya tayarwa mutane da yawa hankali saboda gaskiya a halin da muke ciki yanzu a jihar Borno wato maganar wanda aka kashe a ce ko Musulmi ko Kirista gaskiya wannan ma bai taso ba. A yanayin da muke ciki ire-iren wadan nan maganganun zasu iya kusan raba kawunan mutane...A jihar Borno abun da ya damu gwamna Kashim Shettima ran dan Najeriya mazaunin jihar Borno".
Dangane da ko gwamnan jihar Bornon ya gamsu da yadda hukumomin tsaro ke gudanar da ayyukansu a wannan lokaci tambayar da aka yiwa gwamnan ke nan. Sai yace "Maganar gaskiya shi ne jami'an 'yansanda da na sojoji suna iyakar kokarinsu idan ka dubi irin abun dake faruwa amma ni da kai mun san 'yan Boko Haram sun fisu makamai sun fisu samun kwarin gwiwa. Batun gaskiya a nan shi ne suna iya nasu kokari da irin wannan hali da suka samu kansu ciki.
Gwamnan ya kara da cewa "Ka kalli wadannan mahaukata da kan kona masallatai suna kona coci coci ban san ko za'a iya kiran irin wadannan mutane Musulmai ba ko 'yan ta'ada da mahaukata ban san yadda zan kirasu ba. A don gaskiya ma a kauyen Kawuri sun kona masallatai guda biyar. Kai dangantasu da addinin Islama bai ma taso ba don kuwa wannan ba addinin Islama ba ne don addinin Islama bai yadda wani mahaluki ya dauki ran wani mahaluki ba ba tare da wani dalili ba. Ai wannan cin zali ne kawai kuma muna nan muna addu'a idan Allah Ya yadda abun zai kawo karshe"