Sabon jakaden Ivory Coast a Majalisar Dinkin duniya yace kasar na fuskantar barazanar kisan kare dangi

Mmjoa wa wanachama wa Tuareg akicheza katika kampeni za mkutano wa mgombea urais Ibrahim Boubacar Keita kwenye mji wa Timbuktu Julai 24 , 2013.

Sabon jakaden Ivory Coast a Majalisar Dinkin Duniya yace takaddamar siyasa na iya jefa kasar kisan kare dangi.

Sabon jakadan kasar Ivory Coast a Majamisar Dinkin Duniya ya fada jiya laraba cewa gardamar da ake yi yanzu kan ko wanene ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi a Ivory Coast yana gusawa da kasar ga fuskantar kashe-kashen kare-dangi. Youssoufou Bamba ya yi wannan furuci a birnin New York a lokacin da ya mika takardun kama aikinsa ga babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon. Alassane Ouattara, mutumin da Majalisar Dinkin Duniya da kuma kasashen duniya suka amince da shi a zaman shugaban kasar Ivory Coast, shi ne ya nada Mr. Bamba a matsayin sabon jakadan Ivory Coast a majalisar. Kowanne daga cikin Mr. Ouattara da Laurent Gbagbo dake kan kujerar a yanzu yana ikirarin lashe zaben fitar da gwani na shugaban kasa da aka yi a watan Nuwamba. A halin da ake ciki, ministan matasa da samar da aikin yi na Ivory Coast yayi kira ga magoya bayan Gbagbo da su kwato hotel din da Mr. Ouattara ya kafa hedkwatarsa a ciki a birnin Abidjan inda Majalisar Dinkin Duniya ke gadinsa. Charles Ble Goude yace magoya bayan zasu ‘yanto hotel din Golf a ranar daya ga watan Janairu. Mr. gbagbo dai ya ki sauka daga kan kujerar mulki, kuma Majalisr Dinkin Duniya ta ce an kashe mutane fiye da dari da saba'in a rigimar da ake yi kan wannan mukami.