PLATEAU, NIGERIA - Caleb Mutfwang a jawabin shan rantsuwar kama aiki a matsayinsa na zababben gwamna na shida a jihar Filato, ya ce kusan shekaru ishirin kenan da yankuna daban-daban a jihar musamman a kananan hukumomin Riyom, Bokkos, Barikin Ladi, Bassa, Jos ta Kudu da kuma na kwanannan a Mangu, inda aka auka wa mutane cikin dare aka hallaka fiye da dari.
Ya ci gaba da cewa lamarin da ya haifar da yawan gwauraye da marayu cikin bakin ciki, ya kuma janyo fushi da harzuka zukatan wasu da sunan ramuwar gayya, wanda kuma ya sanya ake ganin al’ummar jihar Filato kamar basa karbar baki, kuma a zahiri, sune ake cuta.
Gwamnan ya ce wadanda ke makwabtaka da jihar Filato dole ne su zauna lafiya da su, su kuma girmama al'adunsu da dabi'unsu.
Mutfwang ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa wajen hada kan al’ummar jihar ba tare da la’akari da yare, addini ko kabila ba.
Daga jihar Nasarawa ma, gwamnan jihar, Abdullahi Sule ya yi alkawarin ci gaba da bunkasa hanyoyin tattalin arzikin jihar, don walwalar jama’a.
Aliyu Ilele Gayam ya ce gwamnan na jihar Nasarawa ya kuma yi alkawarin karasa ayyukan da ya fara.
Shima Yusuf Galadima ya ce gwamnan na jihar Nasarawa ya janyo kamfanoni da za su ba al’ummar jihar ayukan yi.
A jihar Binuwai ma, sabon gwamnan jihar, Rabaran Fada Hyacinth Alia ya yi alkawarin yi wa al’ummar jihar hidima bisa gaskiya da adalci kamar yadda dokar kasa ta tanada.
Saurari cikakken rahoto daga Zainab Babaji:
Your browser doesn’t support HTML5