Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun shugaban hukumar Dr. Ifedayo Adetifa, inda ya kara da cewa babu wani sabon abu dangane da cutar.
Sabbin nau'ikan cutar sun sa kasashe da dama kokarin daukar sabbin matakai wajen bada kariya ga al’ummar su, duba da yadda cutar ta galabaitar da alummar duniya a lokacin da ta bulla a shekarun baya, musamman ta fannin rayukan jama’a da tattalin arziki.
Hakan ya sa hukumomin lafiya a Najeriya suke sa ido don kare yaduwar ta a fadin kasar da kuma samar da kariya ga al’umma.
Kwararren likita a bangaren cututtuka masu yaduwa Dr. Isa Adamu Mavo, yayi karin bayan game da cutar da kuma irin gabobin da cutar take kamawa.
Daraktan tsare-tsare, bincike da kididdiga na hukumar lafiya a matakin farko a Abuja (NPHDA) Dr. Abdullahi Bulama Garba, yace sabbin nau’ikan cutar na corona ba abun tada hankali bane, ya kuma ba da shawarwari kan matakan kariya da ya kamata a dauka.
Dr. Bulama ya kuma kara da cewa rigakafin cutar ba ya hana kamuwa da cutar amma yana rage tasirin ta a jikin dan adam.
Har yanzu dai ana ganin cewa ba a murmure daga karayar tattalin arziki da annobar corona ta haddasa ba a baya gashi kuma ta kara kunne kai da wani sabon salo.
Saurari rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5