An gudanar da taron ne don bullo da wasu hanyoyin da dabarun inganta karbar allurar rigafin cutar ta COVID 19 ga al’ummar kasar sakamokon
Duk da cewa Najeriya na da yawan al’umma sama da miliyan dari biyu an samu wadattacen rigakafin cutar ta covid 19 da aka kawo kasar, sai dai ya zuwa yanzu dai kashi 2.6 ne kawai na adadin wadanda suka karbi cikakken rigakafin da ake bukata, dalilin da yasa cibiyar ta CITAD gayyato kwamishoinin lafiya daga jihohi 19 na arewacin kasar zuwa Abuja don bayyana kalubale da nasarorin da jihohinsu ke fuskanta yayin aikin ba da allurar rigakafin.
Yunusa Zakari Ya'u babban shugaban cibiyar ta CITAD yace rashin fahimta ne ko kuma kishi da ke tsakaninsu ma'aikatu da hukumomin ya yi janyo koma baya, ya kamata sun zauna su fahimci juna.
Jihar zamfara wacce ke da yawan al’umma sama da miliyan 9 na daga cikin jihohin da suka samu nasara wajen samun adadi masu yawa na wadanda suka karbi allurar rigakafin corona duk kuwa da matsalolin rashin tsaro da jihar ke fuskanta kamar yadda kwamishinan lafiyar jihar Aliyu Abubakar tsafe ya bayyana. Bisa ga cewar shi, zamfara na cikin jihohin da suke kan gaba cikin jihohin Arewacin kasar. Ya ce sun yi tsari cikin watanin ukun nan na shekarar 2022 za su yi wa mutane fiye da miliyan 2 allurar rigakafin.
A watan Janairu ne gwamnatin kasar Amurka ta bada tallafin alluar rigakafin corona na Pfizr miliyan 3.2 ga Najeriya sai kuma a litinin din nan data gabata ne gwamnatin Najeriya ta amshi kyautar allurar rigakafin covid 19 na Johnson and Johnson karo na farko daga kungiyar tarayyar turai miliyan biyu a kasar. Kuma ya zuwa yanzu jihar Nassarawa ita ke kan gaba wajen mafi yawan adadin mutanen da suka karbi allurar rigakafin cutar a fadin Najeriya.
Saurari cikakken rahoton a cikin sauti: