Ruwan Sama Na Kashe Gobarar Dajin California Tare Da Wata Barazana Ta Daban

CALIFORNIA-WILDFIRES/

Amma ruwan sama kama da bakin kwarya a kan gaɓar tsaunuka da suka kone, na iya kawo barazanar sabbin matsaloli kamar malalowar toka mai guba.

Ruwan saman da ya fara sauka a busasshiyar kasar Kudancin California za su taimaka wa ma'aikatan kashe gobara wajen dakile harsunan gobarar daji da dama.

Amma ruwan sama kama da bakin kwarya a kan gaɓar tsaunuka da suka kone, na iya kawo barazanar sabbin matsaloli kamar malalowar toka mai guba.

Ma'aikatan gundumar Los Angeles sun kwashe tsawon mako suna kawar da tarkacen itatuwa, da share fili, da kuma karfafa hanyoyi a wuraren da gobarar Palisades da Eaton suka lalata.

Hukumar Kula da Yanayi ta Kasa ta fada jiya Asabar cewa galibin yankin na iya samun kusan inchi daya na ruwan sama a cikin kwanaki da yawa, to amma "barazanar ta kai matsayin a yi mata shirin ko ta kwana," na samun ruwan sama sosai da zai iya haifar malalowar laka da tarkace daga kan tsaunuka.