Hamas ta ambato sunayen mata hudun a jiya Juma’a da Karina Ariev, Daniella Gilboa, Naama Levy, da kuma Liri Albag. Dukkan mata hudun sojojin Isra’ila ne da aka sace su daga tungar soji dake kudancin Isra’ilan a ranar 7 ga watan Oktoba, 2023, lokacin da Hamas ta kaddamar da hari.
Ofishin firai ministan Isra’ila Banjamin Netanyahu ya tabbatar da samun jerin sunayen mutanen ta hannu wakilai masu shiga tsakani kuma zai maida martani daga baya.
Yau da rana ne ake sa ran muasayar fursinonin zata fara. A ranar 19 ga watan Janairu, ranar farko ta tsagaita wutar, Hamas ta sako wasu matan Isra’ila 3 a wata muasayar da aka sako fursinonin Falasdinawa 90.
A fuskar farko ta yarjejeniyar tsagaita wutar, ana sa ran Hamas zata sake mutane 33 da take garkuwa da su a wata musaya da zata kai ga sakin fursinonin Falasdinawa dake tsare a Isra’ila da kuma kara shigar da kayayyakin jin kai da ma janye sojojin Isra’ila daga wasu sassan Gaza.
Yaki tsakanin Isra’ila da Hamas ya fara ne sakamakon harin da Hamas ta kaddamar a kan Isra’ila, inda kungiyar ta ‘yan bindiga ta kashe mutane 1,200 kana ta yi garkuwa da wasu 250.
A wani harin martani da Isra’ila ta kai a Gaza, ta kashe sama da mutane 47,000, a cewar ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza, wadda bata bambance tsakanin farar hula da mayakan kungiyar ba amma a baya ta ce sama da rabin adadin wadanda aka kashen mata ne da yara.
Harin martanin na Isra’ila ya kuma raba sama da adadin al’ummar yankin da muhallansu kana ya lalata wurare da dama a yankin.
Dandalin Mu Tattauna