Harin bam da aka kai a asibitin Saudiyan da yammacin jiya Juma’a, ya yi sanadiyar lalacewar ginin asibitin inda ake bada kulawar gaggawa, majiyar tana fadawa kamfanin dillancin labaran faransa na AFP, wadda ta nemi a sakayata domin jin tsoron ramuwar gayya.
Nan take ba iya gano wani bangare na rikicin Sudan ne ya kaddamar da wannan hari ba.
Tun cikin watan Afrilun shekarar 2023 ne ake gwabza yaki tsakanin sojojin Sudan da sojojin sa kai na RSF, wadda suka yi nasara kwace kusan bakin dayan yankin Darfur dake yammacin kasar mai fadin kasa.
Sun yi wa El-Fasher kawanya, babban birnin jihar Darfur ta Arewa, tun cikin watan Mayu, amma dai sun gaza ayyana kwace birnin, inda wata kungiyar ‘yan bindiga mai kawance da sojin kasar ta sha korasu baya.
A cewar majiyar lafiyar, wani harin jirgi mara matuki na sojojin RSF ya afkawa wannan ginin, a ‘yan makwanni da suka shude.
Ana yawan samun hare hare a kan asibitoci a El-Fasher, inda kungiyar likitocin jin kai ta Doctors Without Borders ta fada a wannan wata cewa asibitin na Saudiya shi kadai ne asibitin jama’a da ya rage da ake gudanar da tiyata.
An tilasta rufe kashi 80 cikin dari na asibitoci a fadin kasar, a cewar alkalummar da aka fitar a hukumance.
Wannan yaki ya kashe dubun dubatan mutane, ya kuma raba sama da mutane miliyan 12 da gidajensu kana ya jefa wasu miliyoyi cikin tsananin yunwa.
Dandalin Mu Tattauna