Fittacen hamshakin attajirin nan mai harkar sadarwa Rupert Murdock ya nemi ahuwa a wata sanarwa da aka buga a jaridun Birtaniya daga wadanda jaridar News of the World ta saci bayanan wayoyinsu da kuma abin fallasar da ya shafi ba ‘yansanda cin banci. A cikin wasikar da Murdoch ya rattabawa hannu wadda aka wallafa yau asabar, ya bayyana nadamarshi da kuma ta kamfanin sabili da laifin da aka aikata da bakin cikin da ya janyowa mutanen da wadansu daga cikin manema labaranshi suka saci bayanan wayoyinsu da kuma biyan ‘yansanda domin samun bayanai. Murdoch ya nemi afuwan ne bayan murabus da Les Hinton ya yi a matsayin shugaban kamfanin sadarwar na Amurka Dow Jones jiya jumma’a sabili da abin fallasar. Hinton ya yi murabus ne sakamakon rawar da ya taka lokacin da yake shugabancin jaridun da kamfanin ke wallafawa a Birtaniya da suka hada da News of the World, lokacin da ‘yan jarida a wurin suke satar sauraron hirar mutane ta wayar tarho.
Rupert Murdock ya nemi afuwa daga wajen wadanda aka saurari hirarsu ta wayar tarho a sace
Fittacen hamshakin attajirin nan mai harkar sadarwa Rupert Murdock ya nemi ahuwa a wata sanarwa da aka buga a jaridun Birtaniya daga wadanda jaridar News of the World ta saci bayanan wayoyinsu da kuma abin fallasar da ya shafi ba ‘yansanda cin banci.