Rundunar 'Yansandan Jihar Taraba Ta Tsaurara Matakan Tsaro

Alhaji Abubakar Sani Danladi, mukaddashin gwamnan Taraba

'Yansandan jihar Taraba sun dauki tsauraran matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama'a a lokutan bukukuwan kirsimati da sabuwar shekara

Kakakin rundunar 'yansandan jihar Taraba ASP Joseph Kwaji shi ya bayyana dalilan tsauraran matakan tsaron da rundunar 'yansandan ta dauka a jihar Taraba.

Rundunar ta dauki matakan ne domin kare rayuka da dukiyoyin jama'a a yayin da ake bukuwan sallar kirsimati da ta sabuwar shekara.Yace an baza 'yansanda a duk fadin jihar. Misali ranar kirsimati 'yansanda zasu kasance a kowace mijami'a inda kiristoci zasu taru su yi sujada.

Kakakin ya kira jama'a da su zauna lafiya. Ya gargadi iyaye su ja kunnuwan 'ya'yansu kada su fita suna kunna abun wasan wuta da ake kira knockout a turance. Yace duk wanda aka samu yana sayarwa ko kuna abun to ko 'yansanda zasu cafkeshi.

Yankin Ibi a kudancin jihar na cikin yankunan dake fama da yawan tashin hankali da ake daidaitawa da addini ko kabilanci. Shugabannin yankin sun kira al'ummarsu su yafewa juna kana su yi cudanya tare. Alhaji Abdullahi A. Ibrahim Dan Masanin Ibi yace masarautar Ibi tana shirya taron sasntawa da kuma kawo fahimtar juna. Su kan yi taruka da shugabnnin addini kana sun kafa kwamitocin yin sulhu. Yace da zara wasu kabilu sun samu matsala da juna kwamitin nan da nan zai shiga tsakani ya yi sulhu. Ya kira a yi hadin kai a manta da banbance banbance a zauna lafiya.

Ita ma majalisar dokokin jihar ta bukaci al'ummomin jihar su rungumi zaman lafiya. Ishaya Gani shugaban kwamitin yada labarai na majalisar dokokin jihar yace duk addinan biyu wato musulunci da kiristanci sun koyas da zaman lafiya. Yace su da a Wukari basu san banbancin addini ba domin a gida daya sai a samu musulmai da kirista. Idan musulmai na bikin salla tare suke cin abinci. Haka ma idan kiristoci na bukin sallah. Yace basu san yadda aka yi ba guguwar banbancin addini ta shigo jihar Taraba ba.

Ga Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar 'Yansandan Jihar Taraba Ta Tsaurara Matakan Tsaro - 3' 09"