Duk da shirin da ake yi akwai wasu da dama da basu yi tanadin komi ba sabili da yanayin da suka samu kansu a ciki.
Da masu gudun hijiran, sanadiyar rikicin Boko Haram, da wadanda suke cikin gidajensu tamkar daya suke domin rashin kudi da kuma rashin biyan albashin ma'aikata a jihar. Mutane basa iya sayen kaya a kasuwa domin babu kudi. Kudin shiga motoci ma ya haura sabili da haka babu tafiya.
Wasu sun ce kamata yayi wadanda suke cikin gidajensu su tuna da wadanda aka rabasu da nasu muhallan sabili da rikicin da ya rutsa dasu.
Shugabannin al'ummomi sun fara kira da ayi anfani da bukukuwa kaman na kirsimati da sabuwar shekara wajen kawo fahimtar juna domin a samu zaman lafiya. Alhaji Abama Kwacam daya daga cikin shugabannin al'ummar yankin Mubi yace kiristan arewa da musulmin arewa suna wasu rigingimu, suna kashe kansu da kansu amma daga karshe dole su dawo su fahimta cewa aikin banza suke yi. Bai kamata a yadda wasu suna shiga tsakanin addinan biyu ba. Rikicin Michika da Madagali ya tarwatsa kowa da kowa. Duk an gudu, musulmai da kirista din.
Kwacam yace dole ne mabiya addinan biyu su hada kansu su sani cewa duk abun da ya faru zai shafesu gaba daya. Duk abun da ake yi domin mulki ne ba domin wani abu ba ne. Ya kira mutane su kare mutuncinsu da mutuncin addinansu a zauna lafiya. Da Alla yana son kasar Najeriya ta zama ta musulmai kawai ko ta kirista kwai da yayi hakan. Amma Allah ya hada 'yan Najeriya hakan ne domin ya nuna ikon mulkinsa.
Da can ba'a san wani banbanci ba ko na addini ko na kabilanci.
A Taraba ma wani dan siyasa Usman Baba Kachalla kuma shugaban al'umma yace zasu yi anfani da bukukuwan su fadakar da jama'a akan illar yin anfani da addini ko kabilanci a harkokin siyasa. Da ma 'yan siyasa ne ke anfani dasu da zara lokacin zabe yayi. Yace ana yin siysa ne domin cigaba amma 'yan tsiraru ne suke haddasa rikici domin cimma nasu muradun. Su ne suke haddasa kashe-kashe da kone-kone. Yace zasu dakile aukuwar irin hakan a zaben shekara mai zuwa.
Ga karin bayani.