Bindigogi guda 110 ne da suka hada da kirar A-47 da albarusai 81 rundunar 'yan sandan jihar Neja ta ce ta kwato daga hannun jama'a a jihar.
A wani taron manema labarai, kakakin rundunar ASP Abubakar Dan Inna ya ce akasarin bindigogin da albarusan wadanda suke rike dasu ba akan ka'ida ba suka dawo dasu sakamakon damar da 'yan sandan suka bayar na yin hakan ba tare da fuskantar hukumci ba.
Akwai wasu kuma da 'yan sanda suka kai samame bisa ga tsegunta masu da aka yi suka kwato bindigogin. Irin mutanen da aka samu makamai gidajensu tuni aka gurfanar dasu gaban shari'a.
Rashin nuna mutanen da suka dawo da bindigogin ya hana Muryar Amurka damar tattaunawa da wasunsu.
Amma gwamnatin jihar ta ce ta yi maraba da ci gaban da aka samu ta fusakar tsaro. Kakakin gwamnan jihar Jabril Baba Ndaci ya yi fatan mutane zasu bi dokar da aka bayar domin dorewar zaman lafiya.Ya kira jama'a da su ba jami'an tsaro da gwamnati hadin kai domin zaman lafiya ya tabbata.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5