Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Neja Na Binciken Mutuwar Wani Matashi


Jami'in NSCDC, ko Civil Defense
Jami'in NSCDC, ko Civil Defense

A jihar Neja 'yan sanda na binciken mutuwar wani matashi a hannun hukumar NSCDC karo na uku a jihar da irin wannan lamari ke aukuwa

Rundunar 'yan sandan jihar Neja tana binciken hukumar tsaro ta Civil Defense, NSCDC, akan mutuwar wani matashi Luka Makana da aka ce ya mutu ne a hannun hukumar a garin Bangi dake karamar hukumar Mariga.

Joseph Tanko mahaifin Luka ya ce jami'an tsaron farin kayan sun daure matashin ne suka dinga dukarsa har ya mutu. Civil Defense din dai ta zargi matashi ne da satar diyan mangwaro guda biyar. Ta bakinsa a cikin daji ne suka iske matashin inda suka kamashi suka kaishi ofishinsu. A nan suka daureshi suka dinga lakada mashi kashi.

Ya kara da cewa suna neman matashin ne sai suka ga 'yan sanda suna fitar da gawarsa daga ofishin Civil Defense. Dangane da ko sun tabbatar 'yan Civil Defense ne suka kasheshi, sai Joseph Tanko ya ce "daga ofishinsu aka fito da gawar matashin".

Shi ma kakakin 'yan sandan jihar ASP Abubakar Dan Inna ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma jami'an hukumar suna hannun 'yan sanda kana ana gudanar da bincike.

Amma kodayake jami'in yada labarai na hukumar NSCDC Malam Ibrahim Yahaya ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce ciwon ciki ne ya kashe matashin. A cewarsa babu wanda ya taba shi.

Kawo yanzu wannan lamarin shi ne karo na uku da mutane suka mutu a hannun jami'an NSCDC a jihar ta Neja.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG