Kungiyoyi masu da'awa a jihar Neja sun nuna damuwa matuka akan yadda kayan dake sanya maye suke yawaita a jihar, musamman a manyan biranen.
Wannan al'amarin na janyo karuwar matasa masu muamala da kayan dake haddasa mayen kamar su barasa da miyagun kwayoyi.
Kungiyoyin da'awar dai sun rubutawa gwamnatin jihar wasikar koke dake bukatar gwamnati ta yi wani abu cikin hanzari akan al'amarin.
Alhaji Haruna Musa shugaban gamayyar kungiyoyin da'awa a jihar a cwersa abubuwan da suka bijiro a jihar sun zama masu sabbi domin basu saba ganin haka ba. Sha'anin masha'a da asha sai karuwa suke yi. Wuraren da aka hana sayar da giya yanzu suna sayar da ita.
Baicin hakan mata zauna gari banza sun karu suna taruwa a wurare daban daban. Injishi tunda akwai ma'aikatar da aka dorawa alhakin kula da abubuwan dake faruwa kungiyoyin suka ga yakamata su mika kokensu domin a mikawa gwamnan jihar.
Shi ma mataimakin shugaban kungiyar dalibai musulmi na jihar Yahaya D. Muhammad ya ce kayan sanya maye na iya yiwa ilimin daliban illa tare da gurbata tarbiyarsu.
A ofishin hukumar dake kula da harkokin addinai ne kungiyoyin da'awar suka mika wasikar kokensu inda babban daraktan hukumar Dr. Umar Faruk Abdullahi ya yi masu godiya ya kuma yaba masu saboda suna son al'umma ta gyaru ne.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani
Facebook Forum