Rundunar ‘Yan Sandan Jihohin Ekiti Da Oyo Sun Shiryawa Zaben Gwamnoni

'Yan Sanda a Jihar Rivers, Maris 30, 2015.

A yankunan kudu maso yammacin Najeriya rundunar ‘yan sanda ta ce ta shirya tsaf domin tunkarar zaben gwamnoni da na ‘yan Majalisun jihohi a fadin kasar.

Da yake yiwa Muryar Amurka ‘karin bayani kwamishinan ‘yan sandan jihar Ekiti, CP Asuquo Amba, ya tabbatar da cewa da yardar Allah sun shirya tsaf domin zaben.

Kwamishinan ya ce da farko sun yi nazarin irin ayyukan da suka gudanar da zaben da ya gabata, domin gano irin kura-kuran da suka yi da kuma samo hanyar da za a kauce musu.

Rundunar ‘yan sandan dai ta sha alwashin bayar da tsaro a runfunan zabe da kuma wuraren tattara sakamakon zabe. Haka kuma zasu girke wata runduna ta musamman tare da bayar da lambobin waya na musamman domin a kirasu idan bukatar hakan ta taso.

A can jihar Oyo kuma, kwamishinan ‘yan sanda Shina Olukolu, ya ce zasu kara yawan jami’an ‘yan sanda da za su yi sintiri domin tabbatar da tsaro a lokacin zaben.

Haka kuma kwamishinan ya yi kira ga ‘yan jihar Oyo da su fito su kada kuri’unsu ba tare da jin tsoron wani abu ba. Yanzu haka dai an fara ganin jami’an ‘yan sanda da shirin ko ta kwana domin ganin an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Hassan Umaru Tambuwal.

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar ‘Yan Sandan Jihohin Ekiti Da Oyo Sun Shiryawa Zaben Gwamnoni - 2'05"