Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Jihar Filato, Jami’iyyar PDP Ta Zargi Jami’iyyar APC Da Shirin Yin Magudi


Jam'iyyar APC
Jam'iyyar APC

Jami’iyyar PDP a jihar Filato ta zargi jami’iyyar APC da kokarin yin magudi a zaben gwamna da na ‘yan majalisun dokokin jiha da za’a gudanar ranar Asabar mai zuwa.

Shugaban jami’iyyar PDP a jihar Filato, Damishi Sango yace sun sami bayanan dake cewa APC na kokarin kwashe kayan zabe daga babban bankin tarayya dake birnin Jos, duk da shike shugaban bankin ya ki amincewa da shirin su.

Sakataren jami’iyyar APC a jihar Filato, Alhaji Bashir Musa Sati, ya ce jam'iyyar PDP na shure-shure ne kawa wanda baya hana mutuwa.

Mai ba gwamnan jihar Filato shawara kan harkokin ma’aikata, Malam Jibrin Bachir ya ce a yanzu dai jama’ar Filato sai san barka suke saboda ci gaba da zaman lafiya da aka samu a jihar.

Ga karin bayani cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG