Nasara a hukuncin kotun daukaka kara da ya ba wa PDP da dan takarar ta Atiku Abubakar hurumin duba duk takardun zaben shugaban kasa, ya sanya jam’iyyar ajiyar zuciya kan damar tattara karin shaidu don kalubalantar sakamakon zaben.
Justice Abdul Aboki na kotun daukaka kara da ita ce matsayin kotun sauraron kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa, ya yanke hukuncin bukata ta farko ta damar duba takardun zabe.
Amma sauran bukatun na daukar hoto da sanya kwararru su tantance sakamakon ba su samu amincewa ba don hakan ya ba wa masu kalubalen damar da ta wuce kima.
Duk da hukuncin wanda ya nemi takarar shugaban kasa a jam’iyyar APDA Shittu Kabir na fatar Atiku zai janye batun a kotun.
Tsohon mai ba wa shugaba Jonathan shawara kan siyasa Farfesa Rufai Ahmed Alkali da yanzu ya ke jam’iyyar SDP, ya ce matsayar da su ka dauka a 2015 na taya shugaba Buhari murna da kaucewa zuwa kotu ya kawo sabon babi a dimokradiyyar Najeriya.
Idan za a tuna, Atiku ya zayyana sakamakon zaben da ya zo na biyu a yawan kuri’u da cewa ko soja ba za su gudanar da irin zaben marar kan gado ba.
Atiku ya ce “idan ka duba sakamakon zaben a tsanake na 23 ga watan Febrairu, za ka ga lissafin bai yi daidai ba, kamar misali a Borno an samu kashi 82% sun kada kuri’a duk da rashin tsaro….a yankunan PDP kuma an samu karanci ko an ma rage kuri’un.