Rundunar 'Yan Sandan Najeriya Ta Cafke Wani Basarake

Wani Basarake da ya yi kitsa sace kansa da kansa ya shiga hannun jami'an 'yan Sanda kuma an dakatar da shi daga mukaminsa.

Rundunar ‘yan Sandan jihar Legas, ta cafke wani Basarake da ma’aikatan wani kafani da ake zargin su da shirya karyar cewa anyi gargkuwa dasu a jihar Legas domin biyan bukatun kansu.tuni dai Gwamnatin jihar ta Legas ta dakatar da Basaraken daga kan mukaminsa.

Kwamisahinan ‘yan Sandan jihar Legas, Mr. Fatai Owoseni, wanda ya tabbatar da kama Basaraken da kuma shirye shiryen gurfanar dashi a gaban kuliya ya bayyana cewa Basaraken yay hi karya game da batun sace shi da yace anyi a ranar 5, ga watan Yuli na bana.

Kwamishinan ‘yan Sandan yace idan za a iya tunawa a ranar 5, ga watan yulin bana ne aka ce an sace wannan Basaraken, sai dai binciken da rundunar ‘yan Sandan jihar Legas ta gudanar ya nuna cewa Basaraken baya jihar Legas, a ranar da aka ce lamarin ya faru.

Kwamishinan ya kara da cewa binciken rundunar ya nuna cewa akwai wata ‘yar rashin jituwa tsakanin da Sarkin wannan yakin wanda kuma aka dorawa alhakin yin garkuwa ko kuma sace shi wannan Basaraken, a takaice dai bincike ya nuna cewa karya yake kuma hukuma zata dauki matakin da ya dace akansa.

Bada wanna akwai wani bincike da rundunar ‘yan Sanda ke gudanarwa na wasu ma’aikata da sukayi awon gaba da kudin ma’aikatarsu da aka ce su kai Banki, inda daga bisani suka bugo waya suka ce suna hannun masu sace mutane, shima bincike ya nuna cewa karya sukeyi suma yanzu haka suna hannu.

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar 'Yan Sanda Ta Cafke Wani Basarake - 2:53"