Shedkwatar Rundunar Tsaron Najeriya a cewar kakakinta Brigediya Janar Tukur Gusau, na maraba da cafke shi da mahukunta a finland su ka yi, sannan suna fatan za a taso keyarsa zuwa gida.
Gwamnatin Finland ta cafke Simon da wasu na hanun damansa guda hudu bisa zargin tunzura al'umma da kuma ta’addanci.
Bugu da kari, ana zarginsa da laifin samar da kudi, tsarawa da daukar nauyin ta’addanci da ya kai ga kashe mutane a shiyyar kudu maso gabashin Najeriya.
Shi dai simon Ekpa na daga cikin wadanda su ka yi ta kokarin hana gudanar da zabe a shiyyar kudu maso gabas da zama a kan gaba wajen kakabawa mutan yankin dokar zaman gida karfi da yaji.
Sannan ana dora masa alhakin galibin kisan ta’addanci da ake yiwa Jama’a a yankin duk da hujjar neman barkewa daga Najeriya
In za a iya tunawa, tun a baya dai babban hafsan Hafsoshin rundunar tsaron Najeriya ya yi ta fadi tashin ganin kasar Finland ta cafke shi don a maido dashi Najeriya ya fuskanci shari’a.
Saurari cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5