Hukumomin kasar Finland sun kama mai fafutukar kafa kasar Biafra, Simon Ekpa, a bisa tuhume-tuhumen aikata ta’addanci.
Hukumar binciken kasar Finland tace ta bukaci a tsare Ekpa a kan zargin tunzura jama’a su aikata laifi, kuma suka aikata hakan da niyar ta’addanci.
Ana tuhumar Ekpa ne tare da wasu mutanen 4 da zargin daukar nauyin laifuffukan ta’addanci, a cewar sanarwar da ‘yan sandan kasar Finland suka fitar a yau Alhamis.
Duk da cewa sanarwar ‘yan sandan bata ambata sunan Ekpa ba, shafin yanar gizon wata kafar yada labaran kasar Finland, Helsingin Sonamat, ya zayyano sunansa a rahoton daya wallafa game da batun.
Sanarwar ‘yan sandan ta bayyana cewa “bukatar tsarewar nada nasaba da wani binciken aikata laifffuka inda ake zargin wani dan Najeriya mai shaidar zama dan Finland da aka haifa a shekarun 1980 ta tunzura jama’a su aikata laifi, kuma suka aikata hakan da niyar ta’addanci.
A watan Maris da ya gabata ne shelkwatar tsaron Najeriya ta ayyana neman daya daga cikin shugabannin haramtacciyar kungiyar 'yan awaren Biafra, Simon Ekpa, ruwa a jallo.
An wallafa sunan Simon Ekpa a jerin sunayen mutanen da hukumomin sojan Najeriya ke nema tare da wasu mutum 96 suka fito daga sassan kasar daban-daban.
A jikin wani kwali me dauke da hotunan mutanen da ake tuhuma, shelkwatar tsaron tace ta ayyana sunayen mutane 97 da take nema ruwa a jallo saboda laifuffukan ta'addanci da tsattsauran ra'ayi da barazanar ballewa daga najeriya.
Dandalin Mu Tattauna