Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Tayi Watsi Da Karar Nnamdi Kanu Kan Tauye Hakki


Nnamdi Kanu da lauyoyinsa (Channels TV)
Nnamdi Kanu da lauyoyinsa (Channels TV)

Mai Shari’a Omotosho, yace Kanu ya gaza gabatar da gamsassun hujjojin da zasu tabbatar da ikirarinsa na hana shi ganawa da lauyoyinsa ba tare da tarnaki ba.

Mai Shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya dake Abuja yayi watsi da karar take hakkin bil adama da jagoran kungiyar ‘yan awaren Biafra (IPOB) dake tsare, Nnamdi Kanu, ya shigar akan gwamnatin tarayya.

Nnamdi Kanu ya maka antoni janar na tarayya da Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) a kotu yana neman diyar Naira bilyan guda akan zargin tauye masa hakkokinsa.

Jagoran kungiyar ‘yan awaren ta ipob yayi ikrarin cewar Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) da shugabanta sun tauye masa hakkinsa na samun shari’a mai adalci ta hanyar hana shi ganawa da lauyoyinsa ba tare da wani tarnaki ba sa’ilin da yake tsare a hannunsu a shirye-shiryen kare kansa daga tuhumar aikata manyan laifuffuka da yake fuskanta.

Yayin da yake yanke hukunci, Mai Shari’a Omotosho, yace Kanu ya gaza gabatar da gamsassun hujjojin da zasu tabbatar da ikirarinsa na hana shi ganawa da lauyoyinsa ba tare da tarnaki ba, ko hana shi yin mu’amala da lauyoyin nasa kai tsaye, kuma jami’an hukumar dss nayi masu labbe duk sa’ilin da zai gana da lauyoyin nasa, abinda yace ya tauye masa hakkinsa na samun adalci a shari’a.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG