Rundunar Tafkin Tchadi Ta Kaddamar Da Farmakin Bai Daya Mai Take Operation Lake Sanity

Hoton babban Kwamandan dakarun tafkin Tchadi da kuma wasu kwamandoji biyu daga Nijar da Kamaru a filin dagas

Rundunar kawancen kasashen yankin tafkin Tchadin ta kaddamar  sabon farmaki da zummar kammala kakkabe sauran burbushin mayakan ISWAP da BOKO HARAM  a yankin tafkin Tchadin.

Farmakin wanda ke gudana a wani salo na bai daya ana auna yan ta'addan ne lokaci guda ta dukkannin bangarorin kasashen yankin.

Dakarun tafkin Tchadin sun shaidawa sashin Hausa na muryar Amurka cewa kawo yanzu sun hallaka gomman mayakan ISWAP da BOKO HARAM tare da kwato kayan yaki ire iren manyan bindigogi da harsasai da kuma cafke wasu manyan yan ta'adda goma sha daya a raye, ciki har da kananan yara guda uku.

Da yake karin bayani kan farmakin kakakin rundunar tafkin Tchadin, Kanar Mohammed Dole yace tsarin OPERATION LAKE SANITY ya hada wasu zaratan mayakan kasa da na sama daga sojojin Najeriya da Nijar ta yankin Najeriya. Wato a bangaren malamfatori a Najeriya akwai dakarun Nijar da Najeriya, sannan a Wulgo/Marte akwai dakarun Kamaru da Najeriya,

Kanar Dole yace akwai jiragen yakin dake marawa dakarun kasa, suna aiki tare da kuma dannawa zuwa sansanonin yan ta'addan Boko Haram din.

Ku Duba Wannan Ma Sojojin Najeriya Sun Ce Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 70 A Wani Samame Da Suka Kai Ta Sama

Kanar mohammed dole yace a halin yanzu sun fatattaki mayakan Boko Haram a yankunan Arege, Fotodiya Tumbin Fulani Da Tunbin Rago, daZammari da Shaza daga bangaren gabas sannan dakarun sun mamaye yankunan, yanzu haka babban kwamandan rundunar ta MNJTF ko kuma FMM Janar AK Ibrahin da kansa na can a filin daga.

Tuni mazauna yankin tafkin Tchadin ke nuna gamsuwa bisa irin yadda dakarun ke kara samun nasara da hakan ya basu damar ci gaba da hada hadarsu na noma da kiwo da ma kamun kifi da kuma zirga zurga tsakanin kasashen, a cewar Abdulkarin Abbas wani mazaunin yankin,

Saurari cikakken rahoto cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar Tafkin Tchadi Ta Kaddamar Da Farmakin Bai Daya Mai Take Operation Lake Sanity