NASARAWA, NIGERIA - Babban hafsan sojan kasa Laftanar Janar Faruk Yahaya ya bayyana haka a taron kaddamar da rijiyar da a ka karawa da na’urar ba da wuta ta janareta don kara karfin hanyoyin samun lantarki.
Faruk Yahaya wanda daraktan sashen mulki na rundunar Manjo Janar OW Ali ya wakilta, ya ce rundunar na da muradun da irin wannan aiki zai shawo kan mutane su rika kaunar soja don hakan ya taimaka wa soja ga gudanar da ayyukan su.
Babban hafsan ya kara da cewa rundunar ta gina makarantar sakandaren koyon ilimin fasaha a yankin.
Da ya ke jawabi daraktan sashen hulda da jama'a na sojoji da farar hula na rundunar sojan Manjo Janar Markus Kangye ya ce da zarar samun bukatar da su ka yi ta neman a tona rijiyar, sun zo sun duba inda ba bata lokaci su ka turo ‘yan kwangila da su ka duba kuma su ka zo su ka tona rijiyar.
Shugaban Hukumar Mulkin Cigaban yankin Yunusa Adamu Mwai wanda tsohon soja ne da ya yi amfani da damarsa ta rashin kin jinin soja, ya bukaci sauran al’ummomin da su ke kusa da wata cibiyar soja su nemi irin tallafin.
Sarkin Mada da ke da fadarsa a garin Akwanga Da Chun Samson Gamu Yaren, ya ce hakika rijiyar za ta taimaka wa jama’ar yankin da samun ruwan sha mai tsafta, inda ya yi amfani da damar wajen bukatar saukaka ma 'ya'yan farar hula kudin karatu a sakandaren kamar yanda a ke yi wa 'ya'yan sojoji.
Da Chun ya mika kyautar kwari da baka ga babban hafsan da ke alamta gwarzanta ta kabilar Mada inda kuma ya ba shi sarautar tauraron Mada.
Saboda yanayin soja na saurin fushi da ma wuce gona da iri, su kan kasance a zaman doya da manja da yawancin jama’ar kasa da mutane ba sa sha’awar hulda da su, don wani lokacin maimakon in an gansu za a samu taimako sai hakan ya kare da cin zarafi.
Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-Hikaya:
Your browser doesn’t support HTML5