Rundunar da ta faro farmakin ne ranar ashirin da daya ga watan Maris, kawo yanzu inda kimanin mayakan ISWAP da Boko Haram dari takwas ne ta hallaka a zirin yankin tafkin Chadin.
Da yakewa manema labaru karin haske a birnin N'djamena, wani hafsan mayakan kasar Kamaru Navy Captain Jiotsa Guy dake zama jagoran sojojin J3 na gamayyar dakarun kasashen yankin tafkin Chadin ya ce dakarun kazalika sun kuma kwato motocin yaki na 'yan ta'addan guda arba'in da hudu, babura, kekuna da kuma boma-bomai goma sha bakwai.
An kuma cimma wannan ne a hare hare guda goma sha bakwai ciki har da farmaki goma sha uku da aka kaiwa maboya ko sansanonin yan ta'addan.alkaluman da yace lalle akwai abin lura a ciki.
Da kuma yake bayanin yadda aka cimma irin wannan gagarumar nasara, Navy Captai Jiotsa ya ce a baya shekaru biyu da suka wuce dakarun na MNJTF suna kare sansanoninsu ne yayin kuma da ‘yan ta'addan ke cin karensu ba babbaka a tsibiran tafkin Chadin dama hamadar dake yankin.
Wannan yasa aka bullo da wani sabon tsari da salon yaki na kai farmaki har tungar ‘yan ta'addan, abin kenan da ake tayi yau watanni biyu kenan kuma koma baya shida kadai dakarun suka fuskanta, wanda shi dinma a makon farko na kaddamar da farmakin ne. Abinda hakan ke nufi shine kwanaki sittin da akayi ana kai samame babu koma baya ko daya da aka fuskanta.
Navy Captain Jiotsa ya ce aiki cikin hadin kai da fahimtar juna ya taka rawa wajen cimma nasara ga wannan gagarumar nasara da aka samu.
Saurari rahoto cikin sauti daga Hassan Maina Kaina:
Your browser doesn’t support HTML5