Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar mayakan ruwan Najeriya Navy Commodore Ayo Voughan ya aikewa sashin Hausa na Muryar Amurka, yace jirgin mayakan ruwan mai suna NNS PATHFINDER ya kai wani farmaki inda ya rugurguza haramtattun wuraren tace man fetur guda goma sha uku, manyan randunan adana mai guda shida da kuma karin wasu manyan tankokin aje man guda biyu duk a jihar Rivers.
Kazalika wani jirgin ruwan sojin ya kuma kara lalata wani haramtaccen wurin tace man a Warrin jihar Delta haka dai mayakan ruwan daya bayan daya sukai ta gano tare da kai farmaki duk wuraren da ake tafka aika aikar satar mai safararsa ko tace shi ba bisa ka'ida ba.
Rundunar sojojin ruwan ta hada jimlar alkaluman da ke nuna ta hana Najeriya yin hasarar kimanin Naira milyan dubu da miliyan dari tara da dubu dari biyar da Naira dubu ashirin da shida da dari shida ta hanyar satar gurbataccen man.
In za a iya tunawa, tun lokacin da ya karbi jagorancin rundunar sojojin ruwan kasar Vice Admiral Auwal Zubayru Gambo ya sha alwashin dakatar da sata da safarar gurbataccen mai da ma fashin teku bisa ga dukkan alamu kuma kwalliya na biyan kudin sabulu.
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5