Wannan na dauke ne cikin sanarwar da mai magana da yawun rundunar Kanal Muhammad Dole ya fitar ranar Alhamis a inda ya ce matan an sace su tsakanin shekarun 2020 da 2021.
Matan dai sun fito ne daga jihohin Yobe, Gombe da Adamawa, a inda tuni suna asibiti don duba lafiyarsu tare da ci gaba da bincike kafin a mikasu hannun gwamnati.
Sunayen matan sun haɗa da Grace Daniel ‘yar shekaru 38, Suzan Lazarus ‘yar shekaru 28, Jumai Inuwa shekaru 42, Maria Adamu 27, Martha Malu 27 da kuma Malakalya Dambade 37.
Sanarwar ta kara da cewa sojoji sun yi nasarar kashe ‘ƴan Boko Haram da dama a yayin da soja daya ya rasa ransa, wannan nasara ta samu ne biyo bayan bayanan sirri da rundunar ta samu a kan wurare irin su Tumbun Fulani, da Tumbun Rago a inda aka kashe ‘yan ta'adda akalla ashirin.
Rundunar ta kara da cewa ta gano wasu gawarwakin ‘yan Boko Haram da dama.
[Alhassan Bala ya bada gudummuwa a rubuta wannan rahoton.]
Saurari rahoto cikin sauti daga Hassan Maina Kaina:
Your browser doesn’t support HTML5