Rundunar Dakarun Tafkin Chadi Ta Cafke ‘Yan Boko Haram 800 Akan Iyakar Najeriya Da Nijar

Rundunar Sojojin Nijeria Sun Sha Alwashin Cigaba Da Farautar Yan Boko Haram

Babban kwamandan rundunar dakarun kawancen yankin tafkin Chadi Manjo Janaral Abdul Kalifa Ibrahim da kuma ake kira AK, ya yi wa Muryar Amurka karin haske kan cafke 'yan kungiyar Boko Haram sama da dari takwas da suka yi a baya-bayan nan.

Janar AK Ibrahim yace ‘yan Boko Haram din da suka hada da mata da yara, sun tsere ne daga cikin dajin Sambisa da nufin zuwa zirin Tafkin Chadi. Na'urorin tattara bayanai da sintiri a sama na rundunar sojan ne suka nuna yadda ‘yan kungiyar ke tururuwar zuwa yankin inda aka kama su.

Babban kwamandan yace sun kama ‘yan boko haram din ne a kan iyakar Najeriya da Nijar a daidai yankin kogin Komadugu/Yobe, a wasu unguwanni da ake kira Garin Dogo da kuma Laskero, inda sojojin Najeriya da Nijar na rundunar MNJTF suke.

yan boko haram

Wadanda aka kama, da yawansu ya kai dari takwas kuma galibinsu ‘yan Najeriya ne, an kai su sansanin sojojin Najeriya da ke garin Gaidam a jihar Yobe, daga bisani kuma aka wuce dasu zuwa Damaturu daga nan aka kai su Maiduguri a jihar Borno.

Da yake amsa tambaya kan ko me ya sa ake ganin ‘yan Boko Haram da yawa na guduwa daga dajin Sambisa a baya-bayan nan, babban kwamandan dakarun kasashen na yankin tafkin Chadi ya ce wannan bai rasa nasaba da yadda sojojin rundunar Operation Hadin Kai ke kai farmaki ta sama da kasa ba kakkautawa a dajin, da kuma mummunan rikicin da ke kara ta'azzara tsakanin bangarorin ‘yan ta'addan ISWAP da asalin kungiyar Boko Haram.

Saurari rahoton Hassan Maina Kaina:

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar Dakarun Tafkin Chadi Ta Cafke ‘Yan Boko Haram 800 Akan Iyakar Najeriya Da Nijar