Ronaldo Da Benzema Sun Yi Ruwan Kwallaye, An Tashi Kunnen Doki

Ronaldo a gasar Euro 2020

Sakamakon wannan wasa na nufin dukkan kasashen biyu, sun shiga zagayen ‘yan 16 da iyawar kowa za ta fisshe shi.

Dan wasan Portugal Cristiano Ronaldo da takwaran karawarsa na Faransa Karim Benzema sun zira kwallaye biyu-biyu a fafatwar da suka yi a gasar cin kofin nahiyar turai ta Euro 2020.

Dukkan kwallayen hudu da aka zira a wasan illa daya, ta hanyar fenarti aka zira su inda Ronaldo ya fara cin kwallon farko a minti na 31.

Amma Benzema ya farke kwallon shi ma ta hanyar fenarti – kusan a nan take.

Sannan jim kadan bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Benzema ya sake zira wata kwallon bayan da Paul Pogba ya doko masa ita ta tsakiyar masu tsaron gidan Faransa.

Ana cikin wasan Portugal ta kara samun wata fenarti wacce Ronaldo ya sake bugawa ta shiga ragar Faransa, abin da ya kai wasan ga 2-2.

Sakamakon wannan wasa na nufin dukkan kasashen biyu, sun shiga zagayen ‘yan 16 da iyawarsu za ta fisshe su.

A wannan rukuni na ‘F’ da ake mai kallon na mutuwa ne, Faransa ce ke jagorantarsa, sai Jamus da ita ma ta yi kunnen da doki da Hungary da ci 2-2 sannan sai Portugal wacce ta kare a mataki na uku.

Yanzu Portugal za ta kara da Belgium yayin da Faransa za ta kara da Switzerland a wasanni na gaba.

Ronaldo yana atisaye da abokanan wasansa na Portugal gabanin karawar da za su yi da Faransa

Your browser doesn’t support HTML5

Ronaldo yana atisaye da abokanan wasansa na Portugal gabanin karawar da za su yi da Faransa

Ronaldo: UEFA Ta Gargadi ‘Yan Wasa Da Su Daina Gusar Da Kwalaben Abubuwan Sha

Your browser doesn’t support HTML5

Ronaldo: UEFA Ta Gargadi ‘Yan Wasa Da Su Daina Gusar Da Kwalaben Abubuwan Sha