“Ya zama dole mu mutunta shawarar da ya yankewa kansa, muna kuma mika godiyarmu da irin kwarewarsa, himma da shaukin aiki da mu da ya nuna mana cikin shekarun da ya kwashe.” Madrid ta ce a wata sanarwa a ranar Alhamis.
Kungiyar ta kara da cewa, “ Zidane, na daya daga cikin jaruman Real Madrid, kuma tarihin da ya bari zai wuce abin da ya cimma a matsayinsa na koci da dan wasa a kungiyar.
Wasu majiyoyi sun fadawa ESPN cewa a ranar Laraba Zidane ya yanke shawarar ajiye aiki a kungiyar wacce ke buga wasa a gasar La Liga da ke kasar Spain.
A ranar Asabar Real ta buga wasanta na karshe da Villareal inda ta lallasa ta da ci 2-1, amma hakan bai ba ta damar ta wuce Atletico Madrid ba, wacce ta lallasa Real Valladolid da ci 2-1 ta lashe kofin gasar a bana.