Zaben mutumin da ya cancanci a damkawa ragamar shugabancin kawancen FDR ya haddasa rarrabuwar kawuna a tsakanin magoya bayan jam’iyyun adawa.
Yayinda wasu ke ganin tsohon shugaban kasa MAHAMAN OUSMAN ne ya kamata ya hau wannan kujera wasu kuwa cewa suke AMADOU BOUBAKAR CISSE ne ya fi cancanta.
INITNIKHAR ALHASSAN na daga cikin masu ra’ayin a baiwa CISSE shugabancin. Yace Cisse mutum ne wanda babu inda bashi da alaka a kasashen duniya. Saboda haka shi ne zai iya jagorancin adawar kasar.
Sai dai mutumin da aka damkawa ragamar wannan sabuwar tafiya bai halarci taron sanarwar ba
To amma Alhassan ya ce ya karbi shugabancin da ba haka ba da basu kirashi taron nadin ba. Shirin bulaguro ne ya hanashi halartar taron .
Rashin aminta da wannan matsayi ya sa wasu kusoshin jam’iyyar MODEN LUMANA nuna bacin rai a fili.
Alhamis idan Allah ya kaimu daya bangaren na FDR zai fitarda sanarwa a hukunce akan wannan sabuwar badakala inji wata majiya. To amma BALA IBRAHIM wani matashin dan siyasa dake MODEN LUMANA ya ce duk wand zai zama dan takara na FDR kamata ya yi ya fito daga gungunsu. Yace har yanzu bai ji wanda MODEN LUMANA ta tsayar ba ya nemi shUgabancin FDR. A tashi fahimtar sai kawancensu ta fitar da wani kana za su je su yi zabe.
Sai dai wani jigo a kawancen adawa ANNABO SOUMAILA na cewa akwai hanyar sasanta wadanan bangarori domin baiwa ‘yan uba kunya.
Wannan shine karon farko da rarrabuwar kawuna ke bayyana a fili karara tsakanin ‘yan adawa a wani lokacin da wasu ‘yan Nijer ke zargin shuwagabaninta da gazawa wajen gwagwarmayar ganin an tsayarda mulki nagari kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya dorawa ‘yan hamayya nauyi a kowace kasar demokradiya.
A saurari rahoton Souley Barma
Your browser doesn’t support HTML5