Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabuwar Kungiyar Yaki Da Ayyukan Da Ke Mayar Da Hannun Agogo Baya a Nijar


Wasu masu sayar da kayayyakin marmari kusa da kogin isa ko Neja.
Wasu masu sayar da kayayyakin marmari kusa da kogin isa ko Neja.

A jamhuriyar Nijar, wasu kungiyoyin fararen hula sun bada sanarwar kafa gungu da zummar yaki da miyagun ayyukan da ke barazanar maida hannun agogo baya wajen wanzar da damokradiyya, sannan sun lashi takobin yaki da masu cin hanci da handamar dukiyar jama’a.

Ta hanyar wani kwarkwaryan biki ne wadannan kungiyoyi suka bada sanarwar kafa gungun Forum de LA Societe Civil Nigerienne Pour Un Niger Nouveau;

Kungiyoyin da suka hada da ANC da OVUL da ANPD na cewa halin da ake ciki a yau a Nijar an kai matsayin da za a sake sabuwar tafiya domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a Nijar sabuwa.

"Mu kokawar da muke yi domin kasarmu ta bunkasa, talaka ya zamanto an tausaya mashi game da tafiyar da mulki. Kuma ya zamanto ba mutane kalilan ne ke babakere da dukiyar kasa," inji jagoran wannan hadaka, Dakta Bubakar Amadou Hassan.

Ya ci gaba da cewa, "Muna so ne a shimfidar da dimokradiyya da doka, duk wanda bai da gaskiya in aka gurfanar da shi a gaban kotu, a ba shi rashin gaskiyarshi, mai gaskiya kuma a bashi kuma babu wanda zai zamanto zai taka doka a ce wai don kana tare da iko, wato kai bai yiwuwa a tuhumeka wancan a tuhumeshi."

Domin fayyacewa ‘yan Nijar bambancin tsarinta da na sauran gungun kungiyoyin da aka saba kafawa a wannan kasa, hadakar FSCN ta fara yi wa ‘yan siyasa hannunka mai sanda kamar yadda sakatarenta Dambaji Son Allah ya bayyana.

'Wannan kungiyar da muka kafa ba kungiya ba ce wadda 'yan siyasa za su ce za su yi amfani da ita. Mu ba mu tare da 'yan siyasa na adawa ko na iko,"

Rashin jituwar da ke tsakanin bangarorin siyasar Nijar akan maganar shirye-shiryen zabe na daga cikin abubuwan da ke daukar hankalin wannan sabuwar hadaka.

Yanzu haka hankalin jama’ar Nijar ya karkata wajen kotun Yamai domin jin hukuncin da alkali zai yankewa wasu masu fafutuka a wata shari’ar da ke cike da cece-kuce saboda haka, sabon gungun na FSCN ya gargadi alkalan shari’a cewa kada su saurari dukan wani katsalandan ko wata barazana akan aiki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG