Alhaji Tanko Babbo Abbo Andami, daya daga cikin manyan sarakunan gargajiya na yankin Karim Lamido kuma daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa, ya ce a cikin dare da misalin karfe biyu suka samu labarin harin har an kashe wani yaro, dayan kuma sai da aka kai shi asibiti ya cika.
Maharan sun yi kone-kone a kauyuka akalla bakwai, lamarin da ya sa wasu mazauna kauyukan gudun hijira zuwa cikin garin Jalingo fadar mullkin jihar Taraba.
Rundunanr ‘yan sandan jihar Taraba ta tabbatar da faruwar rikicin da ya yi sanadin mutuwar mutanen biyu da kuma kone-kone, kamar yadda kakakin rudunar SP Usman Abdullahi ya bayyana.
Alhaji Ahmed Umar Karim, dan asalin garin Karimjo ne kuma daya daga cikin wadanda suka shaida lamarin, ya ce rikicin ya samo asali ne sakamakon nadin Sarkin Wurkun da gwamnatin jihar da ta wuce ta yi bayan mutuwar tsohon Sarkin.
Hon. Muhammad Audu, dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Ardo Kwala Lau da Karim Lamido a Majalisar Wakilan tarayyar Najeriya, ya yi kira ga dukkan bangarorin biyu da su yi hakuri su kai zuciya nesa domin a samu a kawowa yankin ci gaba mai dorewa da zaman lafiya.
Saurari cikakken rahoton Lado Salisu Garba:
Your browser doesn’t support HTML5