Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar Garkuwa Da Mutane Na Karuwa A Jihar Bauchi.


Yan bindiga a jihar Sokoto
Yan bindiga a jihar Sokoto

Matsalar ‘yan bindiga dake kaddamar da hare-hare da kuma satan mutane don neman kudin fansa a jihar Bauchi na ci gaba da ta’azzara.

A cikin mako guda ‘yan bindigan sun kaddamar da ayyukan ta’addanci a yankunan kananan hukumomin Ningi da Jama’are inda suka kashe mutane da kuma satan masu sarautun gargajiya da kuma ‘yan kasuwa.

Hari na baya bayan nan shi ne wanda ‘yan bindigar suka kaddamar a kasuwar garin Jama’are, hedkwatar karamar hukumar Jama’aren dake jihar Bauchi, inda suka sace wani hamshakin dan kasuwa da kuma yin harbin kan mai uwa da wabi da ya janyo sanadiyar rasa ran wani matashi da kuma illata wassu mutanen.

Kakakin rundunan ‘yan sandan jihar Bauchi,SP Muhammed Wakil, ya yi karin haske kan batun inda ya ce lamarin ya faru ne da dare inda wasu bakin haure suka zo da dama cikin kasuwar Jama’are su ka yi ta harbe-harbe cikin iska har su ka yi garkuwa da wani dan kasuwa.

Ya kara da cewa bayan kwamishinan ‘yan sandan na Bauchi ya samu labarin lamarin, ya umarci rundunar ‘yan sanda ta yi duk abun da za ta yi wajen gano wadannan bata garin.

Shugaban riko na karamar hukumar Jama’are, Malam Inuwa Mosha shi ma ya shaida cewa ‘yan bindigan masu tarin yawa ne suka shigo kasuwar a kan Babura.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG