Rikicin Cikin Gida Ya Kunno Kai a Jami'yyar APC Mai Mulki - Dalung

Solomon Dalung

A Najeriya rikici ne ya ke neman kunno kai a jam'iyyar APC mai mulki lamarin da ya kai ga wasu sanannun 'yan jam'iyyar suka fara kokawa da yadda shugaban jam'iyyar mai rikon kwarya kuma Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni ke tafiyyar da jam'iyyar.

Daya daga cikin jigajigan jami'yyar APC mai mulki kuma tsohon Ministan matasa da wasanni Barista Solomon Dalung, ya koka kan cewa akwai rikicin cikin gida da ke haramar barkewa nan ba da jimawa ba. Ya kuma ce rikicin ya na da nasaba da kokarin mallakar jam'iyyar gabanin zaben shekarar 2023.

Solomon Dalung ya zargi wasu Gwamnoni guda 3 wadanda ke mulki a yanzu haka da cewa suke kokarin neman shugabancin jam'iyyar a shekarar 2023.

Duk da cewa Dalung bai ambaci sunan kowa ba amma ya ce matakin da suka dauka na sake fasalin jam'iyyar ya sa a yanzu babu wani mutum daya da zai fito ya ce shi dan jam'iyyar APC ne, domin shugabannin rikon kwaryar jam'iyyar sun rusa dukkanin mukamai tun daga gundumomi har zuwa matakin tarayya, sannan sun ce za a sabunta rajistar jam'iyyar wacce za ta kunshi sunayen 'yan jam'iyyar a kasa baki daya.

Dalung ya ce yanzu hakan na nufin shi kanshi Shugaba Buhari ma ba dan jam'iyya ba ne domin ba a riga an yi masa rajista ba balle ya samu katinsa na zama dan jam'iyya.

Amma tsohon shugaban kwamitin tsare-tsare na jam'iyyar Ibrahim Masari, ya ce akwai mumunar rashin fahimta a yadda jam'iyyar ta ke gudanar da harkokinta a yanzu, domin matakin da aka dauka na rusa shugabanni masu mukami a jami'yyar daga matakin gunduma zuwa tarayya, ba ya na nufin cewa an rusa ko kuma an kori 'yan jam'iyyar ba ne.

Masari ya ce duk dan jam'iyya har yanzu dan jam'iyya ne kuma su na da katunansu na zama 'yan jam'iyya, babu wanda ya isa ya rusa su.

To sai dai ga mai fashin baki a al'amuran yau da kullum Mustapha Shehu Ruma, ya ce dama siyasa ta gaji irin wadannan kananan rikice-rikicen amma kuma su ne suke karfafa jam'iyya, matukar ana taka-tsantsan wajen bin dokokin tsarin mulkin jam'iyyar.

Abin jira a gani shi ne yadda za ta kaya a lokacin taron kasa da jam'iyyar ke haramar yi a wani lokaci nan gaba kadan.

Saurari cikkaken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Rikicin Cikin Gida Ya Kunno Kai a Jami'yyar APC Mai Mulki - Dalung