Suna barazanar bujurewa duk zabukan dake tafe muddin ba'a biyasu diyar irin asarar da suka yi ba a rikicin da ya biyo bayan zaben 2011.
Alhaji Abubakar Sadiq Dahiru, daya daga cikin wadanda suka kira manema labaru a jihar Kaduna domin nuna damuwarsu, yace makasudin taron nasu shi ne su kokawa gwamnatin tarayya kasancewa jihar nada al'ummomi daban daban da kuma wasu banbance.
Rikicin 2011 da ya biyo bayan zabe ya haifar darashin dukiyoyi da gidaje da ma rayuka. Shugaban kasa ya sanya kwamiti ya binciki lamarin su tantance abubuwan da aka yi asara. Dalili ke nan suka tara duk wadanda abun ya shafa daga jihar kasancewa kawo yanzu jihohi tara sun anfana daga rahoton kwamiti din. Jihohin an biyasi diya amma su sun ji shiru.
Zaben 2011 ya haddasa matsalar da suke ciki yanzu kuma ga wani zaben yana karatowa, sabili da haka suke kokawa. Suna rokon gwamnati tayi wani abu ta kuma dubesu da idon rahama. Yayin da suka gana da sakataren gwamnatin tarayya sai ya nuna masu an samu matsala ne a jihohin Kaduna, Gombe da wasu shi yasa aka samu tsaiko.
Alhaji Sani Uba, sakataren sarkin Husawan Zonkwa yana daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa. Yace su wakilai ne na jama'a idan kuma za'a yi zabe na gaskiya sun isa su sa mutum ko ya ci zabe ko ya fadi. Basu ga dalilin da yasa an mayar dasu saniyar ware ba. Suna da mataimakin shugaban kasa wanda daga jihar ya fito amma sai gashi an ba wasu jihohi diya amma su ba'a basu ba.
Wai kafin Namadi Sambo ya cika alkawarin kawo kuri'u miliyan biyu ya gyara lamarin tukunna.
Amma daraktan yada labarun gwamnan Kaduna Alhaji Ahmed Abdullahi Mai Yaki yace babu abun da zasu gayawa al'ummar illa su basu hakuri. Babu abun da za'a yi ya maye rayukan da aka rasa. Mutane suyi hakuri domin abun da ya faru daga Allah yake. Ya kirasu su cigaba da hakuri.
Ga rahoton Isah Lawal Ikara.
Your browser doesn’t support HTML5