Hukumar tace jiya Laraba ya kamata ta rufe aikin raba katin amma sabili da yin la'akari da yawan mutane da basu samu ba ya sa ta kara kwana daya.
Duk da karin jama'ar jihar na korafi matuka da nuna rashin gamsuwarsu da yadda aikin ya gudana.
Tuni dai shugabannin kungiyoyin jama'a suka koka tare da yin kira ga hukumar zaben da ta canza matsayinta. Umar Faruk Abdullahi sakataren limaman addinin musulunci na jihar Neja yace akwai matsala ta cinkoson mutane. Mashinan da ake anfani dasu basu da inganci. A wasu wurare sai a wuni basu yi aiki ba balantana a yiwa mutane rajista a basu katinsu.
Alhaji Shehu Galadima na kungiyar manoman jihar yace akwai wasu da suka yi tsohon rajista. Suna da tsohon katin tare dasu amma sai a nemi sunansu a rasa. Yace samun sabom fam a sake cikawa ya zama matsala. Abun mamaki wasu tun karfe uku na dare aka ce su shiga layi amma duk da haka sun yini basu samu katin ba.
Hatta gwamna Muazu Babangida Aliyu na jihar ya bayyana shakku akan lamarin. Yace "INEC da National Assemby su san cewa babu yadda za'a yi zabe idan suka matsa cewa lallai sai wannan permanent voters card za'a yi anfani dashi. Dole su fito da wata hanya wanda bai samu ba amma yana da rajista dole yayi zabensa."
Hukumar zabe, INEC, tace a yanzu haka mutane miliyan daya sun karbi katin zaben a jihar Neja daga cikin mutane miliyan daya da rabi da aka yiwa rajista a baya. Sauran mutane dari biyar din kuma zasu karbi katunansu ne a ofisoshin hukumar dake kananan hukumomi. Ta kira jama'a da su kwantar da hankalinsu domin babu wani shiri na hada kai da ita domin yin magudi.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.