Rigakafi AstraZeneca Nada Kaifi Wurin Dakile Yaduwar COVID-19-Oxford

Rigakafin AstraZeneca

Sakamakon wani bincike da Jami’ar Oxford ta fitar yau Laraba ya nuna cewa maganin rigakafin korona birus da kamfanonin AstraZeneca da Jami’ar ta Oxford suka samar, yana rage yaduwar kwayar cutar da kashi biyu bisa uku.

Ba a kammala tabbatar da sahihancin binciken ba, amma Sakataran Lafiya na Birtaniyya, Matt Hancock ya shaidawa BBC cewa labari ne mai dadi jin.

Hancock ya kara da cewa “Wannan ya nunawa duniya allurar ta na aiki, ta na aiki sosai.”

Wasu kasashen Turai sun soki maganin rigakafin a baya bayan nan, inda wasu jami’ai suka nuna damuwa kan rashin bayar da bayanai game da ingancin maganin a jikin tsofaffi.

Sai dai jagoran masu gwajin allurar rigakafin na jami’ar Oxford, Andrew Pollard ya ce duk da ba su da isassun bayanai, maganin ya na aiki yadda ya kamata, allurar rigakafin tana bada kariya ga garkuwar jikin tsofaffi.

Babbar kungiyar bada shawarwari a kan kiwon a Faransa ta bada shawarar anfani da rigakafin a kan mutanen da suke kasa da shekaru 65 kadai.

A Belgium, gwamnatin kasar ta ce zata yi allurar rigakafin ga wadanda ke kasa da shekaru 55 kadai.

A New Zealand, yau Laraba ne hukumar kula da harkokin kiwon lafiya ta tabbatar da amfani da rigakafin Pfizer da BioNTech na wucin gadi.