Ribadu Ya Yi Barazanar Maka Shugaban PDP A Kotu Kan Zargin "Bata Masa Suna"

Mai ba da shawara kan sha'anin tsaron kasa, Mallam Nuhu Ribadu (Hoto: Facebook/NTA)

Sai dai a wata wasika da ya aikawa shugaban jam’iyyar a ranar 15 ga watan Satumbar 2024, Ribadu ya nemi Aziegbemi da ya janye kalaman nasa inda ya kwatanta lamarin a matsayin “zuki ta malle”

Mai ba da shawara kan sha’anin tsaron kasa (NSA) a Najeriya, Mallam Nuhu Ribadu ya yi kira ga Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Edo, Anthony Aziegbemi da ya yi gaggawar janye zargin da ya yi cewa yana yukurin murde zaben gwamna da za a yi a jihar.

A ranar Asabar 21 ga watan Satumba za a gudanar da zaben gwamna a jihar ta Edo da wacce ke kudu maso kudancin Najeriya.

Rahotanni daga Najeriyar sun bayyana cewa cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar Aziegbemi ya zargi Ribadu da jagorantar tsara wasu hanyoyi da za a murde zaben.

Ya kara da cewa Ribadu ya bai wa dan takarar APC a zaben, dala miliyan biyu don a tsara a kuma aiwatar da magudin.

Sai dai a wata wasika da ya aikawa shugaban jam’iyyar a ranar 15 ga watan Satumbar 2024, Ribadu ya nemi Aziegbemi da ya janye kalaman nasa inda ya kwatanta lamarin a matsayin “zuki ta malle”

Lauyar Ribadu Marian Aigbedion ta ofishin lauyoyi na Charles Musa and Co, ta ce “wannan mummunan kazafi ya jefa kwastomanmu cikin yanayi na tsangwama da yake fuskanta daga jama.”

Kazalika Ribadu ya nemi a biya shi diyyar Naira biliyan 10 a kuma rubuta tallan neman afuwa a akalla jaridu guda biyar.

Jam’iyyar APC mai mulki a jihar ta tsayar da Sanata Monday Okpebholo a matsayin dan takararta a zaben mai cike dsa takaddama yayin da jam’iyyar PDP ta tsayar da Asue Ighodalo.

Gwamna Godwin Obaseki na shirin kammala wa’adinsa na biyu a matsayin gwamnan jihar.