Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mashawarcin Shugaban Najeriya Akan Harkokin Tsaro Ya Bada Umarnin Tursasa Aiwatar Da Dokar Yaki Da Laifuffukan Intanet


Mashawarcin Shugaban Kasa Akan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu
Mashawarcin Shugaban Kasa Akan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu

Mashawarcin Shugaban Kasa Akan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, ya bukaci a aiwatar da dokar yaki da laifuffukan intanet ta bana da aka yiwa kwaskwarima (tun daga rigakafi har izuwa haramci), ciki harda kyale hukumomin sa ido da kamfanoni su ci gajiyar gidauniyar yaki da laifuffukan intanet ta kasa kamar yadda aka fayyace a cikin dokar.

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun Shugaban, Sashen Yada Labarai Ma Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasar Akan Harkokin Tsaro, Zakari Mijinyawa, tace umarnin wani yunkuri na bada kariya ga tsarin sadarwa na kasa (CNII), da yaki da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi da karfafa tsaron kasa da kuma kare muradan tattalin arzikinta.

A ranar 6 ga watan Yulin 2022, Najeriya ta shiga sahun kasashe 66 da suka kulla yarjejeniyar birnin Budapest akan yaki da laifuffukan intanet tare da maida ita doka domin karfafa hadin kan kasa da kasa, da samar dandali da tsarin aiwatarwa bai daya domin samar da sahihiyar sadarwar intanet mai cike da tsaro karkashin sashe na 41(2) na dokar yaki da laifuffukan intanet ta 2015, wacce ke bukatar dacewar da dokoki da manufofin Najeriya akan tsarin da kasashen Afirka dana duniya suke tafiya game da yaki da laifuffuka da tabbatar da tsaro a kafar sadarwar intanet.

Sanarwar ta kara da cewar, daya daga cikin kudirorin da aka cimma yayin wani taron kolin Afirka akan yaki da laifuffukan intanet tsakanin kasa da kasa, daya gudana a Abuja tsakanin ranaikun 22 da 23 ga watan Afrilun daya gabata, hakan ya kara fitowa fili.

Kudirin ya bukaci samun karin goyon baya da kudade, domin karfafa ayyukan yaki da laifuffukan intanet a nahiyar Afirka, tare da daukar kwararan matakan da zasu kange ‘yan ta’adda da kungiyoyin miyagu daga amfani da kafafen sada zumunta.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG