Real Madrid Ta Koma Jagorantar Teburin Gasar La Liga

'Yan wasan Real Madrid suna murna

Madrid ta samu wannan nasara ce duk da cewa da ‘yan wasa 10 ta buga wasan

Dan wasan Real Madrid Lucas Vazquez ya zura kwallon da ta ba kungiyarsa damar darewa teburin gasar La Liga na kasar Sifaniya.

Madrid ta doke Alaves da ci 1-0 bayan da Girona ta tashi da ci 1-1 da Real Betis.

Madrid da Girona sun yi kunnen doki da maki 45 a teburin gasar ta La Liga.

Madrid ta samu wannan nasara ce duk da cewa da ‘yan wasa 10 ta buga wasan.

Alkalin wasa ya sallami Nacho Fernandez bayan da aka same shi da laifin yin shigar keta.