Rayuwa Karkashin Dokar Ta Baci

Wani ke nan yana neman abun da zai iya tsinta a juji domin ya sayar ya samun kudin kalaci

Rayuwa Karkashin Dokar Ta Baci: Muryar Amurka ta shirya tattaunawa kan yadda dokar ta baci da aka kakabawa jihohi uku na arewa maso gabashin Najeriya suka shafi rayuwar yau da kullum na al'ummominsu
Muryar Amurka ta shirya tattaunawa game da yadda dokar ta baci da aka kakabawa jihohi uku na arewa maso gabashin Najeriya suka shafi rayuwar yau da kullum na al'ummominsu.

An fara tattaunawar a jihar Adamawa, jihar da ake gani bata cancanci a kakaba mata dokar ba. An gayyato mutane daga sassa daban daban. Akwai 'yan kasuwa maza da mata, da masu sana'ar daukar fasinjoji da babura da aka sani da suna acaba, da 'yan jarida, da ma'aikatan kiwon lafiya, da jami'an gwamnati, da masu sharhi kan harkokin yau da kullum da dai makamantansu.

Mutane sun fadi albarkacin bakinsu game da yadda dokar ta shafi rayuwarsu. A fannin masu dafawa da sayar da abinci lamarin ya yi masu muni. Da wuya su sayar da kimanin kashi daya cikin goma na abun da suka saba sayarwa kafin kafa dokar. Masu aikin kiwon lafiya na fuskantar matsala da jami'an tsaro wajen zuwa aiki da dawowa. Marasa lafiya basa samun kulawar gaggawa idan suna bukata domin babu hanyar sadarwa da za'a yi anfani da ita a gayyato likita. Dauko marasa lafiya ko daga kauye ko cikin gari zuwa babban asibiti na samun tangarda. Sau da yawa marasa lafiya sun mutu a hanyarsu ta zuwa asibiti domin jami'an tsaro sun bata masu lokaci. Lamarin bai bar masu nakuda ba ko jarirai da yara. Yawancin jami'an tsaro suna buge da giya abun da ya sa basa aiki cikin cikakken hankali.

'Yan jarida sun fuskanci matsalar zagayawa su taro labarai a kan kari. Sau da yawa basa iya kaiwa inda zasu dauki labaru inda sun ji kishin-kishin. Gargadin da jami'an tsaro suka basu na cewa su tuntubesu idan sun ji wani abu basu iya aiwatarwa ba domin babu hanyar sadarwa. Idan ma wani abu na faruwa da ya bukaci gaggawa babu abun da zasu iya yi domin ba wayar hannu ko kuma wata hanyar sadarwa.

Amma duk da matsalolin jami'an gwamnati sun ce dokar ta zama dole ne domin a dakile irin tashin-tashinar da jihar ta samu kanta ciki. Sun yi harsashen cewa da kura ta lafa kuma an tabbatar da tsaro za'a dage dokar. Sun ce ba nufin gwamnati ba ne a kutuntawa jama'a.

Bakin masu tattaunawar ya zo daya game da hadin kai da al'ummar Adamawa ta wa jami'an tsaro tun lokacin da sarakunan gargajiya da shugabannin addini da gwamnati suka jama jama'a kunnuwa suka rokesu su goyi bayan dokar. Tun lokacin matasa suka hada kai. Babu wanda ya tayarwa kowa hankali. Sun ce matsalar Adamawa ta cikin gida ce. Babu wanda ya fito daga wata kasa ko wani wuri ya kawo masu tashin hankali.

Daga karshe wadanda suke cikin zauren tattanawar sun yi kira ga gwamnati ta yi ma dokar ta bacin sassauci domin mutane su samu walwala musamman yayin da watan azumi ke karatowa. Sun ce kamata yayi a cire dokar domin mutane su samu su rika zuwa tafsiri lokacin azumi. Sun yi magana da kakkarfar murya a dawo da hanyar sadarwa domin ita ce tafi shafar rayuwa. Rashin tarho ya hana 'yan jarida watsa labaru kamar yadda ya kamata. Idan akwai matsala wani wuri ta tsaro ko ta rashin lafiya babu yadda za'a aika da sakon gaggawa. Mutane suna rayuwa a takure..

Wakilinmu ya shirya cikakken rahoton kalamun mutane.

Your browser doesn’t support HTML5

Rayuwa Karkashin Dokar Ta Baci-36.42